Hukumar ƙaallon ƙafa ta duniya wato FIFA ta fito da sabuwar dokar data bayyana cewar ɗan wasa yana da damar sauya ƙasa domin fafata wasan ƙwallon ƙafa, hukumar ta bayar da wannan dokar ne bayan yin taronta datayi karo na 70.
Tuni wasu ‘yan wasan suke barin ƙasarsu ta haihuwa domin komawa wata ƙasaf mawai don su buga wasan ƙsallon ƙafa, sai dai mafi yawa ‘yan wasan nahiyar Afrika sun fi yawan komawa wasu ƙasashen musamman ƙasashen turai.
Sai dai wani hanzafi ba gudu ba ita kanta hukumar ta bayar da wasu sharuɗa akan hanyoyin da ɗan wasa ya kamata yabi kafin ya koma zuwa wata ƙasar, sai hukumar tace idan ɗan wasan zai sauya tofa ya tabbata sai ya buga wasanni uku kuma banda gasar cin kofin duniya.
Haka zalika hukumar ta ce amma iya ‘yan wasan da suke da shekaru 21 kawai suke da damar sauyawa daga wata ƙasar zuwa wata. Ita dai FIFA tana ta fitar da wasu dokokin data kafa kuma a yanzu gananan zata sake fito da wasu dokokin