Wani ɗan wasan ƙwallon kafa na Najeriya ya kwanta dama bayan ya faɗi ana tsaka da wasa.
Ado Hadi, mai shekara 21, wanda yake bugawa kulob ɗin CD Madridejos a rukunin Terceira na ƙasar Spain wasa, ya faɗi kawai inda yace ga garin ku nan ana tsaka da wasa tsakanin kulob ɗin sa da SP Cabanillas a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairun 2023.
KU KARANTA KUMA: Daga zuwa neman aurenta, budurwa ta shararawa saurayinta mari a gaban jama’a
A wata sanarwa da hukumar ƙwallon kafa ta Castilla-La Mancha, ta fitar, an bayyana cewa ɗanwasan ya faɗi ne ba tare da wani dalili ba a minti 35 na wasan. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
Jami’an kula da lafiya dake a filin wasa sun garzaya domin bashi taimakon gaggawa, amma ƙoƙarin da suka yi na farfaɗo da shi bai yi nasara ba, inda ƴan mintoci kaɗan ya rigamu gidan gaskiya.
Ado Hadi kafin tafiyarsa ƙasar Spain, ya takawa kulob ɗin Jigawa Golden Stars wasa a nan gida Najeriya.
Kafin mutuwar sa, Hadi yana ɗaya daga cikin ƴan Najeriya huɗu waɗanda yanzu haka suke taka leda a CD Madridejos.
Kulob Deportivo Madridejos wani kulob ɗin ƙwallon ƙafa ne wanda yake a Madridejos, Castile-La Mancha a ƙasar Spain.
Ɗan Wasan Man United Ya Samu Mummunan Rauni, Zai Kwashe Dogon Lokaci
A wani labarin na daban kuma, ɗan wasan tsakiya na Manchester United, ya samu rauni, zai kwashe dogon lokaci bai taka leda ba.
Akwai yiwuwar ɗan wasan tsakiya na kulob ɗin Manchester United, Christian Eriksen, ba zai sake buga wasa a wannan kakar ba ssboda raunin da ya samu.
Ɗan wasan na ƙasar Denmark mai shekara 30 a duniya ya samu raunin ne a yayin wasan da Manchester United tayi da Reading a gasar kofin FA na Ingila.
Man United ta bayyana cewa zai jinyar sa zata tsawaita wacce ka iya kai wa har zuwa ƙarshen wata Afrilu ko farkon watan Mayu.