Ɗarururuwan Ɗaliban Jami’ar Adekunle Ajasin dake Akungba Akoko, Jahar Ondo sun fito daga Makarantar domin gudanar da zanga-zanga akan yawaitar haɗurra a cikin garin, da manyan motoci.
Wannan zanga-zanga dai ta faru ne a dalilin mutuwar abokin su, wanda ake kira da Micheal a ranar Alhamis, wadda Tirela ta markaɗe shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matsalar Tsaro: Mun gaji da Kashe mu da ake yi kullum — Ƙungiyoyi 400 sun gayawa Gwamnatin Tarayya
An ruwaito cewar bayan kashe shi, Direban motar yayi ƙoƙarin guduwa amma akan kama shi tare da miƙa shi ga ƴan sanda dake yankin.
Masu zanga-zangar dai sun cika bakin Makarantar, inda suke akan babbar hanyar Owo-Ikare Akoko, suna waƙoƙi na nuna sadaukarwa a gareshi.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, zanga-zangar na cigaba da gudana, a yayinda jami’an tsaro ke wurin suna ta ƙoƙarin samar wa motoci hanyar da zasu wuce.