Ɗumbin Magoya Bayan APC Sun Shelanta Goyon bayan su ga PDP A Kwara
Ana cigaba da samun cece-kuce a yayin wani taron da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta gudanar a garin Shawo Kudu maso Yamma da ke karamar hukumar Offa ta jihar Kwara, yayin da ‘yan jam’iyyar suka fito ƙarara suka bayyana goyon bayansu ga jam’iyyar PDP ba tare da son APC ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓen 2023: INEC zata fara ɗaukar Ma’aikatan Wucin Gadi
Hotunan faifan bidiyo da suka fito daga taron jam’iyyar APC, sun nuna yadda shugaban Jam’iyya da mataimakinsa suka yi kokarin hana mambobin jam’iyyar rera wakar PDP a yayin taron amma fusatattun ‘yan kungiyar suka bijire masa.
Rahotanni sun ce sun yi wa shugaban gundumar tsawa suna gaya masa cewa dole ne PDP ta dawo kuma Offa ta zama cikakkiyar ta PDP.
Bai ji dadin yadda lamarin ya faru ba, shugaban jam’iyyar APC da ya yi kokarin shawo kan ’ya’yan da suka fusata, ya shaida musu cewa kada su bari PDP ta dawo kan karagar mulki.
Wannan ci gaban na zuwa ne kwanaki hudu bayan da mutanen Oyun suka kori kwamishinonin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq a fusace.
Sun kuma tarwatsa tarurrukan Unguwanni na jam’iyyar APC, ganin cewa gwamnatin da Gwamna Abdulrazaq ke jagoranta, ta gaza wa ‘yan Oyun tun shekaru uku da ya yi yana mulki a jihar.
A wani labarin kuma: Kada ku Zaɓi Atiku, Domin hakan zai wargaza haɗin kan Najeriya — Jigon APC ga Ƴan Najeriya
Wani jigon jam’iyyar APC a jihar Legas, Joe Igbokwe, ya gargadi ‘yan Najeriya game da takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP na Atiku Abubakar.
Igbokwe ya yi gargadin cewa takarar Atiku za ta yi illa ga hadin kan Najeriya.