Jihar Ondo Gidanku Ne Babu Abin da Zai Kara Samunku -Gwamna Fayemi ga Fulani
Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya kuma Gwamnan jihar Ekiti, Fayemi ya bai wa Fulanin dake zaune a jihar Ondo tabbacin cewa babu abin da zai sake samun su. Inda ya ce su kwantar da hankalinsu, jihar Ondo gidansu ne.
Har wala yau ya yi gargadin a daina kabilantar da matsalar tsaron kasarnan, domin a cewarsa, matsalar ta shafi kowacce kabila a Nijeriya.