Wata tankar mai ta sake bindiga, Kimanin Awanni 48 bayan fashewar wata tankar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 12 a Karamar Hukumar Agatu ta jihar Binuwe.
Kamar yadda tankar ta baya ta fashe, Wannan ma kazalika ta sake fashewa ne a kauyen Oshugbudu na Karamar Hukumar Agatu inda ta amsa da wuta yayin da take tsaka da tafiya.
To sai da kamar yadda rahotanni suka bayyana, sabuwar fashewar ta auku ne wannan karo a kusa da ofishin yan sanda.
Amma kuma kamar yadda Shugaban Karamar Hukumar Agatu John Ikwulono ya bayyana, babu asarar rai ko da guda sakamakon wannan ibtila’i.
To sai dai ya ce gidaje da dama sun kone kurmus sai toka, duk da kasancewar ya ce ba su san adadin gudajen da suka konen ba.
Duk da ikirarin Shugaban Karamar Hukumar, amma Hukumar Kiyaye hadura ta Jihar ta ce gidaje biyu ne kachal suka kone.