Daga Mukhtar Yakubu
A rana Alhamis din data gabata ne 15 ga watan Yulin 2021. aka gudanar da taron tantance jaruman da za su fito a cikin shiri mai dogon Zango mai suna Birnin Dala.
Shirin wanda kamfanin Kumbo zai dauki nauyin shirya shi, kuma nan da dan wani lokaci za’a shiga aikin shi, don haka aka yi taron tantance jaruman da za su ta ka rawa a cikin sa.
A kalla jarumai kusan dari uku ne suka halarci wajen tantancewar, da aka gudanar a dakin taro na Darrul-tauhid da ke kan titin Zaria, a cikin garin Kano.
Asalin shirin dai wasan Kwaikwayo ne aka fara gabatar da shi, a gidan Rediyon Dala F M Kano, wanda kuma bayan karbuwar shirin aka fadada shi ya koma fim.
Tsawon lokacin da aka shafe ana gabatar shirin a rediyon dai, ya samu karbuwa sosai a cikin Kano da ma garuruwan da su ke kusa da ita, wannan ya sa duk lokacin da a ke gabatar da shirin ya ke samun dumbun masu sauraro.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babbar Salalh: Hukumar NSCDC ta baza jami’an 1750 domin tabbatar da tsaro a jihar Kano
Fim din dai ya tabo Sarautar Gargajiya, da kuma yadda tsarin Sarauta ya ke a kasar Hausa, hakan ne ya sa jama’a da dama su ke mayar da hankali wajen sauraron sa.
Abin jira a gani dai shi ne, yadda za a gudanar da aikin fim din da kuma karbuwar sa, a wajen masu kallo.