Gwamnatin jihar Kano za ta ba da fifiko wajen horar da mata da matasa a shekarar 2022 a karkashin shirye-shiryenta na karfafa gwiwa musamman a matakin farko.
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma, Dakta Zahra’u Muhammad Umar, ce ta bayyana hakan a lokacin da take kare kasafin kudin ma’aikatar ta 2022 a zauren majalisar dokokin jihar Kano.
Ta bayyana cewa kimanin Naira miliyan 800 da aka ware don tallafawa al’umma an tsara su ne domin magance fatara da rashin aikin yi a matsayin manyan abubuwan da ke shafar rayuwar al’umma.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta tsara dabarun da nufin farfado da noman gida da man gyada da kuma matan karkara ke nomawa a cikin gida domin dogaro da kai.
KARANTA WANNNAN LABARIN: Mutane 5 sun Kone Kurmus Sanadiyar Fashewar Tankar Mai a Hanyar Legas Zuwa Ibadan
Ta ce Cibiyar Reformatory ta Kiru tana ci gaba da gyare-gyare tare da fadada ta domin daukar dimbin masu shaye-shayen miyagun kwayoyi maza da mata domin su zama masu amfani a cikin al’umma.