2023: Ƙungiyar Lauyoyi ta fusata, tayi maganganu kan goyawa Ɗan Takara baya
Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya NBA tayi jawabi kan damuwar da wasu mambobinta ke nunawa na shirin amincewa da goyawa daya ko biyu daga cikin ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen 2023 mai zuwa.
Akpata da yake magana a wani taron Manema Labarai gabanin taron shekara-shekara na 2022 a jihar Legas, ya ce NBA ba ta siyasa kuma ba za ta amince da kowa ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cutar Ƙyandar Biri ta kama mutane 13 a Bayelsa
Akpata ya ce, “Muna so mu nunawa mutane cewa bamu da sha’awa kuma NBA Bata da niyyar goyawa Ɗan Takara ɗaya ko biyu ko uku baya”.
Akpata ya bayyana cewa taron da suka yi, ya karbi bakuncin hudu daga cikin ƴan takarar shugaban kasa na 2023, daya ne kawai daga cikin taron da muke yi, kuma ba ƙudirori ya bayyana ba.
“Ba wai dare ko rana ba ne, zama ne na yau da kullun a taron inda muke yin tambayoyi game da batun dimokuradiyya a lokacin mika mulki da kuma gibin shugabanci da muka gano a ƙasar nan.”
Ya yi nuni da cewa gayyatar da aka yi masa ita ce a bai wa ƴan Najeriya damar sanin shugaban kasa na gaba.
“Duk da haka, mun yi tunanin cewa ya kamata mu tattauna da wadanda ke kokarin neman mu a matsayinmu na ’yan Najeriya, domin mu ba su damar shugabanci.