2023: Ƙwarewar da Kenya ta Nuna, yanzu dole INEC ta canja fasalin Zaɓe
Wata kungiyar farar hula ta Connected Debelopment (CODE), ta ce binciken da ta yi na Babban zaɓen ƙasar Kenya da aka kammala kwanan nan ya nuna cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) na bukatar ta sake duba sa’o’in da take kaɗa kuri’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Majalisar Yobe Sun yi Kakkausan Gargaɗi ga Gwamna Buni akan yawaitar Ambaliyar Ruwa da ake samu
Darakta, Dimokuradiyya da Mulki na CODE, Mr Emmanuel Njoku, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, a taron kaddamar da rahoton shekara-shekara na CODE, inda ya yi bayani dalla-dalla yadda INEC take gudanar da ayyuka daban-daban da kuma kokarin da take yi na tabbatar da gaskiya da rikon amana a Najeriya da Afirka.
A cewarsa, dole a ba da shawarar sake duba sa’o’in zabe na INEC domin idan ba a yi haka ba, za a iya hana sama da mutane miliyan 30 da suka cancanci kada kuri’a a zaben 2023.
Ya ce hakan ya faru ne saboda Kenya ta yi amfani da na’urar Bimodal Voter Accreditation System (BVAS) iri daya kuma tana watsa sakamakonsu ta hanyar yanar gizo kamar Najeriya kuma tsarin kusan iri daya ne, yayin da kawai bambancin ke cikin yadda yawan ƙuri’u ke bayyana.
“Rijistan masu kada kuri’a a Kenya ya kai miliyan 22.1 ne kawai, kuma yawan masu kada kuri’a ya kai kashi 65, wanda ya kai kimanin kuri’u miliyan 14, a Najeriya muna sa ran za a fitar da kashi 45 cikin 100 na masu kada kuri’a, wanda ya kai kusan mutane miliyan 40.
“Amma duk da haka ana bude rumfunan zabe na Kenya da karfe 6 na safe kuma a rufe da karfe 5 na yamma wato sa’o’i 11 na rajistar masu kada kuri’a kasa da miliyan 2.1 abin da ke nufin kowa ya kada kuri’a. Duk da haka, mutanen da ke da yawan kuri’u a Najeriya suna buɗewa na sa’o’i shida kacal daga 8:30 da kuma rufe da 2:30 na rana wato sa’o’i shida kawai na rajistar masu jefa kuri’a na mutane miliyan 95.