Wata kungiyar kula da yanayin mata ta Najeriya (WSRN), da wata kungiyar farar hula (CSO), ta kaddamar da cibiyar gargadi da daukar matakan tunkarar matsalar cin zarafin mata a zaben 2023.
Ko’odinetan hukumar WSRN ta Kasa, Farfesa Joy Onyesoh, ita ce ta kaddamar da cibiyar a Abuja, inda ta ce halin da kasar ke ciki ne ya janyo kaddamar da cibiyar.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Taron ya kasance tare da tallafi daga UN WOMEN da gwamnatin Kanada.
“A cikin shekarun da suka gabata da kuma abubuwan da suka faru a baya, kungiyar ta gano cewa zabe rikici ne wanda ke hana mata shiga harkar zabe,” in ji ta.
A cewarta, WSRN wata kungiya ce ta farar hula ta mata da ta jagoranci yunkurin neman kara yawan shigar mata cikin tsarin siyasa da rigakafin rikice-rikice kamar yadda UNSCR 1325 ta tanada.
Ta ce, “Najeriya ta yi gwagwarmaya a shekarun da suka gabata don hana afkuwar cin zarafin mata (VAWE).
“Daga lura da yadda ake gudanar da zabuka na gama-gari da na fidda gwani a baya, WSRN ta gano cewa cin zarafin mata a zabe kalubale ne kuma yana hana Najeriya gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci. Kamar Yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito
A Wani Labarin Kuma Buhari Yace Tinubu Ne Zai Zama Shugaban Kasa a 2023, Shugaban APC
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce za a zabi dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu ne ya jagoranci Najeriya.
Maganar tasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, Daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC (PCC) ya fitar.