An caccaki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, LP, Peter Obi kan halin mabiyansa.
Deji Adeyanju, wani mai fafutukar siyasa, ya zargi Obi da haifar da ‘yan ta’adda.
Adeyanju ya yi ikirarin cewa mabiya Obi na yi wa ‘yan Najeriya barazanar kisa.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/2023-ko-mutum-200-ba-zaku-samu-a-kaduna-ba-el-rufai-ya-yi-martani-ga-dan-takara/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, A cikin wani sakon twitter, ya koka da cewa mabiyan Obi ba sa jure wa ‘yan adawa, ya kara da cewa suna daukar nauyin labaran karya, mara tushe, da farfaganda a kan wadanda ke da sabanin ra’ayisu.
A cewar Adeyanju: “Peter Obi yana kiwon ‘yan ta’adda da sunan tsayawa takarar shugaban kasa.
“Mutanen da ke yi wa ‘yan kasar barazana da kisa da sunan siyasa sai su ci gaba da cin mutuncin wadanda ke sukar ayyukansu tare da ninka karin farfaganda, karya da labaran karya.”
DAILYPOST