Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce jam’iyyar APC za ta ci gaba da kasancewa tare da dunkulewa wuri guda har bayan wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da shirin a gidan Talabijin na Channels Television wanda DAILY POST ke sa ido a ranar Lahadi.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga rade-radin da ‘yan adawa ke yi na cewa jam’iyya mai mulki za ta Tarwatse bayan shugaba Buhari ya bar mulki a 2023.
Ya bayyana cewa wasu gungun mutane ne suka kafa jam’iyyar APC a bisa dalili kuma shugaba Buhari ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar kuma daga karshe ya ci zabe a 2015.
Ya ce wannan dalili ne zai sa APC ta kasance tsintaiya madaurinki daya
“Na san Shugaba Buhari a yau yana jagorantar abin da ya kamata a yi, don haka Obasanjo haka yake a PDP kuma lokacin da ya tafi jam’iyar ta watse? Don haka, idan Buhari ya bar mulki, APC ma ba za ta yi kasa a gwiwa ba.
“Kuma Buhari zai kasance tare da mu, shi ne shugaban jam’iyyar kuma zai ci gaba da kasancewa tare da mu.
“Kuma wadanda suka yi imani cewa Shugaba Buhari zai je Daura ya kwana, ba su san shi ba, yana da kishin kasa, ya dawo mulki ne bayan ya yi kokari har sau uku saboda yana son al’amura su canja.
“Don haka ba zai nade hannunsa ya bar abin da ya gina ko ya fara ginawa ya watse ko ya lalace ba, kishin kasa a wurinsa, ba zai sa ya bari hakan ta faru ba, don haka muna da shugaba har yanzu,” in ji Badaru.