Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya ce yankin Arewacin kasar nan zai biya dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.
Gwamna Badaru ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Tinubu a Kano ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Ya Bada Tallafin Naira Miliyan 100 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Kano
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC , Ahmed Bola Tinubu, ya ziyarci jihar Kano domin bude ofisoshin yakin neman zabensa.
Gwamnonin jihohin Kano, Jigawa da Zamfara ne suka tarbe Tinubu a ranar Asabar a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano tare da dubban magoya bayansa.
Da yake jawabi ga dimbin jama’ar da suka hallara, Gwamna Muhammad Badaru ya ce Tinibu ne kadai ya goyi bayan ‘yan takarar shugaban kasa biyar na Arewa.
“Tinubu shine abokin arewa daya tilo, ya goyi bayan yan takarar shugaban kasa biyar na arewa da suka hada da Shehu Shagari, Umar Musa Yar’adua, Atiku Abubakar, Nuhu Ribado da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari.”
“Don haka lokaci ya yi da za mu biya kuma mun shirya, mu mutane ne masu gaskiya, muna mutunta alkawari kuma a shirye muke mu biya ku diyya kan abin da kuka yi wa Arewa.”
Gwamna Badaru, ya bukaci ’yan Arewa da su fito su kada kuri’ar zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.
A wani labarin kuma,
Xi Jinping Ya Zarce Wa’adi Na Uku A Tarihi A Matsayin Shugaban Kasar China
Xi Jinping ya samu wa’adi na uku mai tarihi a matsayin shugaban kasar Sin a ranar Lahadi, kuma ya cika da’irarsa da abokan hulda, inda ya samu nasara bayan shafe shekaru goma yana samun cikakken rinjaye kan jam’iyyar gurguzu mai mulki.
Kwamitin tsakiya na jam’iyyar ya zabi Xi a matsayin babban sakatarensa na karin wa’adin shekaru biyar, abin da ya maido da kasar bisa tsarin mulkin mutum daya bayan shekaru da dama da aka shafe ana raba madafun iko tsakanin manyanta.