Kakakin jam’iyyar NNPP, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba zai daidaitu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar sa Sanata Rabiu Musa Kwnakwaso ba.
Jibrin ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today, wanda jaridar Daily trust ta rawaito.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa Kwnakwaso zai lashe kuri’u a Arewa kuma zai samu isassun kuri’u a kudancin kasar nan.
Karanta kuma: Ina Da Tabbacin Yin Nasara Don Haka Bazan Taimakwa Yan Takara Ba
Ya ce, “Dan uwana, Daniel Bwala, ya yi maganar cewa PDP ta kasance a ko’ina, amma ta yaya? A 20215 an ci su a zaben; a 2019 sun sha kashi a zaben. A cikin 2023 har yanzu za a ci su a zagayen zaben. Dan takararsu (Atiku) bai dace da Kwankwaso a yankin Arewacin kasar nan ba.
“Idan aka yi maganar APC, abin da APC ba ta so kowa ya yi magana a kai shi ne yadda su ke lashe duk zabukan da suka gabata saboda sun fara zaben da katin zabe na kuri’u miliyan 12 saboda Buhari. A yau kuri’u miliyan 12 ba sa nan.
“A karon farko cikin shekaru takwas ko shekaru 10 za su fara zaben shugaban kasa da sifili. Ina za su samu kuri’u miliyan takwas? Wannan shi ne abin da shugabannin APC ba su yi magana ba a yanzu. Za su fara daga sifili. A nuna mani mutum daya daga APC wanda zai iya yin tasiri a kan wannan kuri’un kujerun. Ba za su iya samun shi ba. Don haka gaskiyar magana ita ce Kwankwaso ya kulle arewa kuma zai samu isassun kuri’u daga yankin kudancin kasar nan.”
A wani labarin kuma: Amusan Ta Karbi Lambar Yabo Ta, Yayin Da Buhari Ya Karrama ‘Yan Was
Sarauniyar Tobi Amusan a ranar Alhamis ta samu lambar yabo ta Officer of the Order of the Niger (OON) a yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama ‘yan wasan kasar saboda bajintar da suka nuna a gasar da suka fafata.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Bikin da Buhari ya jagoranta ya ga yadda babban kwamanda ya bada Naira miliyan 200 ga tawagar ‘yan wasan Najeriya da za su halarci gasar wasannin Commonwealth da kuma gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya na shekarar 2022. Ya kuma ba su lambar girma ta kasa.