2023: Atiku Ya Saba Shan Ƙasa, Tinubu ne Zai Lashe Zabe – Gwamna Masari
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya bayyana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin gogaggen wanda ya saba faduwa zaɓe.
Atiku wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya sha neman kujerar shugaban kasa amma yana shan kaye.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobara ta hallaka wani Mutum a Asibitin Kano
Wani abin ban mamaki a shekarar 2007, Atiku da Asiwaju Bola Tinubu, daya daga cikin manyan abokan hamayyarsa a zaben 2023, sun hada kai don kwace mulki daga hannun PDP, amma marigayi Shugaba Umaru ‘Yar’adua ya lashe zaben, wanda Atiku, a lokacin shine Mataimakin shugaban kasa ne ya nemi Kujerar Shugaban Ƙasa a karkashin Jam’iyyar Action Congress da Tinubu ya kafa.
Kokarin karshe da Atiku ya yi a zaben shugaban kasa shi ne a shekarar 2019, wanda ya sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari.
Yayin da yake bayyana a wani Shiri na ƴan jarida na Hangout na gidan talabijin na TVC a yammacin ranar Laraba, Masari ya caccaki Ɗan Takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP, inda ya ce, “Atiku babban Mai Karfi ne, amma Tinubu ya fi karfi. Atiku gogagge ne a fafatawar zabe kuma tsohon dan takara ne. Zai sake rashin nasara a hannun Tinubu.”
Masari ya kuma caccaki Peter Obi, Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, wanda ya bayyana a matsayin wanda bai da wani mahimmanci.
“Ban san Obi ba. Mutanen Katsina nawa ne suka san Obi?” Wa ya fi Tinubu? Muna magana ne game da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Najeriya wanda ya yanke kowane shinge, ya shiga ko’ina- kabilanci, yanki da addini.
Da aka tambaye shi ko mutanen Katsina sun yi amanna da Tinubu, Gwamna Masari ya ce, “Tinubu ne zai zama shugaban kasa Insha Allahu. Katsinawa sun son sa. Jama’a sun san rawar da ya taka a shekarar 2015 lokacin da aka zabi shugaba Buhari a kan mulki. Sun san rawar da ya taka a 2019, lokacin da aka sake zaben Buhari. Mu mutanen Katsina bama butulci.”
Masari ya ce matsalolin rashin tsaro da suka addabi wasu sassan jihar ba za su shafi sakamakon zaben 2023 ba.
“Har yanzu APC ce jam’iyyar da za ta doke kowace Jam’iyya. Rashin tsaro ba shine kawai matsalar Najeriya ba. Nijar ba ta da tsaro. Mali ba ta da tsaro, Afirka ta Tsakiya ba ta da tsaro. Akwai matsalar rashin tsaro a duniya,” inji shi.