Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Kasar nan, Mista Usman Baba, ya dora alhakin karuwar rikice-rikicen siyasa da ake samu a kasar kan wasu gwamnonin jihohi.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Baba ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis din nan a Abuja.
KARAMTA KUMA IGP Ya Tabbatar Da Cewa Babu Wata Matsala Ga Babban Zaben 2023
Ya ce an kira taron ne domin jan hankalin shugabannin jam’iyyun siyasa kan yadda ake samun karuwar rikicin siyasar da kuma gabatar da yadda za a magance matsalolin.
“Muna ta samun rahotannin wasu Gwamnonin Jihohi da ke karfafa ‘yan barandan siyasa.
“Suna amfani da kayan tsaro na kananan hukumomin da ke karkashinsu domin dakile ayyukan yakin neman zabe na jam’iyyu ko ‘yan takarar da suke da sabanin ra’ayi na siyasa.
“A don haka, suna amfani da ikonsu da tasirinsu don hana yakin neman zabe ko kuma su ruguza su.
“Suna kuma hana ‘yan adawar siyasa gudanar da yakin neman zabensu ko ayyulansu na siyasa cikin lumana wanda ya saba wa tanadin dokar zabe ta 2022 (Kamar yadda aka gyara),” in ji shi.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa IG ya ce ya dora alhakin mafi yawan tashe-tashen hankula a kan tsattsauran ra’ayi na siyasa, rashin fahimta, rashin hakuri, kuskuren siyasa, kalaman kiyayya, tunzura jama’a da kuma yanke kauna na wasu ‘yan siyasa.
A wani Labarin Kuma Hajjin 2023: Saudiyya Ta Taimakawa NAHCON Kan Shirye-Shirye – Shugaban
Hukumar jin dadin Alhazai ta Kasa NAHCON ta bayyana cewa ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta sanar da shirin gudanar da aikin hajjin shekarar 2023.
Shugaban kuma babban jami’in hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Hassan ne ya bayyana hakan a wajen taron masu ruwa da tsaki na aikin Hajji na shekarar 2022, wanda aka gudanar a dakin taro na masallacin kasa, ranar Alhamis din nan a Abuja.