Tsohon Gwamnan Jahar Borno Sanata Kashim Shettima yace adalci da gaskiya, shiya sanya yankin Kudu dole ya fito da Shugaban Ƙasa mai zuwa.
Shettima na magana ne a taron Ƙungiyoyin Magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu daya gudana a Abuja a ranar Litinin, ya bayyana cewar idan har Shugabancin Ƙasa zai koma Kudu, babu wani a Jam’iyyar APC a yankin dayafi cancanta kamar Tinubu domin jagorancin Ƙasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Chidozie Awaziem ya Soma Atisayi
Ya bayyana cewar yanda Tinubu yayi sadaukarwa sosai a Najeriya, da Jam’iyyar APC lokacin shine daya kamata ya samu.
Haka zalika dayake jawabi a sanarwar daya fitar wanda wata ƙungiya ta fitar a Kaduna, Shettima yace makomar Najeriya ya dogara ne aka mutum irin Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban Ƙasa.
Ya bayyana Tinubu a matsayin Shugaban Shuwagabanni, mutum wanda ya yi ƙoƙari domin ɗora gwamnati maici a yanzu.