Shugaban kasa Buhari ya sanya ‘yan Nijeriyar da suke kasashen waje cikin farin ciki sakamakon nuna goyon bayan Buhari da a bari ‘yan Nijeriya dake kasashen waje suna zaben Nijeriya a inda suke.
Shugaba Buhari ya amince da hakan ne a taron da ya je birnin Addis Ababa dake kasar Habasha a jiya Talata.
Buhari ya ce ba shi da matsala a rika barin ‘yan Nijeriya dake kasashen waje domin gudanar da zabe, inda ya ce idan har ‘yan Nijeriya suna son a rika hakan suna da damar da za su je gaban majalisa ta maishe shi cikin doka.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da ‘yan Nijeriya mazauna kasar Habasha. Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya yi Buhari ya yarda da zaben ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje, amma domin cimma hakan akwai bukatar a maishe shi zuwa doka.