Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya rantsar da sabbin Kwamishinonin Hukumar Zabe mai Zaman Kanta guda 6.
Bikin rantsarwar wanda ya gudana kafin fara zaman Majalisar Zartaswa ta Ƙasa a ɗakin taro a Fadar Shugaban Ƙasa dake Villa Abuja, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da na Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila sun halarci taron, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fifita Adawar Jam’iyya akan Kishin Ƴan Ƙasa, shiya hana APC yin Abinda ya dace — Cewar Wani Matashi a Katsina
Sabbin Kwamishinonin Hukumar Zabe mai Zaman Kanta da aka rantsar sun haɗa da Malam (Niger) da Mrs May Agbamuche-Mbu (Delta) da Ukaegbu Nnamdi (Abia) da Manjo-Janar Abubakar Alƙali ( mai ritaya daga Adamawa), da Farfesa Rhoda Gumus (Bayelsa) da kuma Mr Sam Olumekun (Ondo).
Dayake jawabi bayan rantsar dasu, Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Farfesa Mahmood Yakubu ya bada tabbaci ga ƴan Najeriya na Hukumar domin yin aiki tuƙuru don Babban zaɓe mai zuwa.
Yace “wannan rana ce kyakkyawa ga ƴan Najeriya, da ƙaddamar da Kwamishinoni guda 6, muna da cikakkun Kwamishinoni na Ƙasa guda 12.