Tsohon shugaban Majalisar Dattijai ta Ƙasa Dr Bukola Saraki ya bayyana ra’ayin shi na tsayawa takarar shugabancin ƙasar a Babban Zaɓe Mai zuwa na Shekarar 2023, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaita.
Saraki ya bayyana ra’ayin tsayawa takarar a lokacin da yakai ziyara ga Gwamnan Jahar Benue Samuel Ortom a ranar Talata a Makurɗi, wanda ya bayyana shi a matsayin mutum mai daraja a Jam’iyyar PDP.
A cewar rahoton da majiyar jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito, Saraki ya ziyarci makurɗi tare da tsohon Gwamnan Jahar Kogi Idris Wada, da Tsohon Shugaban Jam’iyya PDP na Ƙasa Kawu Baraje, da kuma Sanata Suleiman Adokwe, gami da Shugaban gangamin yaƙin neman zaɓe na Saraki Farfesa Iyorwuese Hagher.
KARANTA WANNAN LABARIN: Firaminista Mace Ta Farko A Kasar Sweden Zata Jagoranci Gwamnatin
“Jam’iyyar da bazata iya shirya harkokin ta ba, babu dalilin dazai sa ta cigaba da jagorantar Ƙasa. Amma Jam’iyyar data shirya a shirye take ta jagoranci ƙasar, kuma itace PDP,” Inji Saraki.
Ortom a ɗayan ɓangaren ya bayyana cewar PDP zata ceto Najeriya daga Jam’iyya mai mulki ta APC.
Ya bayyana cewar Saraki shine wanda yazo daga Arewa ta Tsakiya dayake ƙwarewa a jagorancin Najeriya a matsayin shugaba.