Babban Bankin Najeriya ta nesanta kanta da rahoton da wata Jarida ta yanar gizo (wadda ba Dimokuraɗiyya ba) datake cewa, Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele, zai ajiye muƙamin sa ya nemi takarar shugaban Ƙasa a shekarar 2023.
Dayake maida jawabi, Mai Magana da Yawun babban Bankin Najeriya Osita Nwasinobi a lokacin tattaunawa sa da Jaridar LEADERSHIP yace wannan rahoton yana kawai kawo tsaiko ne ga abinda Babban Bankin Najeriya yake yi na kula da kuɗaɗen al’umma da goyon bayan shirye-shiryen Gwamnati.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da ɗuminsa: Buhari ya ɗage haramcin yin Twitter, baya shafe watanni 7
“Bansan ina ne inda kafar sadarwa ta yanar gizo ta samo wannan labari ba. Muna tattauna batun kuɗi da yanda zamu taimaki Gwamnati Bama tattauna batun siyasa. Duk waɗannan abubuwa ya kamata su kyale mu domin muyi aikin mu,” inji Nwasinobi.
Rahoton Kafar sadarwa ya ruwaito wata majiya daga Bankin cewa, cewa Emefiele ya shaidawa wasu Mataimakan sa guda 4 cewa, a watan Disamba, zai ajiye muƙamin sa a matsayin Gwamnan Babban bankin Najeriya domin ya nemi Shugaban Ƙasa.
Emefiele yana akan wa’adin mulkin sa na biyu a ofis. Shine Gwamna na farko na Jonathan ya naɗa, kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sake naɗa shi.
Comments 1