Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya bayyana abin da zai yi idan da takwaransa na Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya tsaya takarar Shugaban kasa a Babban zaben shekarar 2023.
Wike ya ce da Ganduje ya tsaya takaran Shugabancin Najeriya, da shi ba zai tsaya takarar ba.
Da yake jawabi yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Ganduje a Kano, dan takarar kujerar Shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDPn, ya bayyana jin dadinsa da cewa Ganduje ba ya cikin masu Neman kujerar.
Ya bukaci takwaransa na jihar Kano da ya goyi bayan aniyarsa ta shugaban kasa a babban zaben shekarar 2023 Mai zuwa.
“Idan Ganduje ya tsaya takarar shugaban kasa wasu daga cikinmu za su yi gaggawar janye burinmu, amma alhamdulillahi bai tsaya takara ba, kuma na tabbata zai taimaka min wajen ganin na Sami nasara,” in ji Wike.
A halin da ake ciki kuma, tun da farko Ganduje ya gargadi Wike game da biyan bukatarsa ta Neman zama shugaban shugaban kasa.
Ganduje ya yi ikirarin cewa Wike zai yi rashin nasara idan ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 dake tafe.
A wani labarin Kuma na daban
Aare Afe Babalola, wanda kuma shi ne shugaban jami’ar Afe Babalola dake Ado-Ekiti, ABUAD, ya shaida wa gwamnati mai ci da ta dakatar da gudanar da babban zaben 2023, ta kuma nada gwamnatin wucin gadi.
Ya ce wa’adin dakatar da zaben shugaban kasa da sauran zabuka zai baiwa kasar damar rubuta sabon kundin tsarin mulkin da ya dace da mutane.
Ya ce sabon kundin tsarin mulkin da gwamnatin rikon kwarya za ta samar nan da watanni shida, zai magance matsalolin rashin tsaro, tattalin arziki, siyasa da sauran munanan cututtuka da suka addabi al’umma.
Babalola ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Ado-Ekiti, inda ya yi gargadin cewa, idan aka bar gudanar da babban zaben 2023, za a sake yin amfani da irin wadannan shugabanni, da kuma kara jefa kasar nan cikin fatara, wahalhalu da rance.
Kalamansa: “Don ceto Najeriya daga shiga cin hanci zuwa cikin fatara da ba za a iya warwarewa ba, barnar tattalin arziki da siyasa da ba za a iya gyarawa ba da kundin tsarin mulkin shekarar 1999 da masu cin gajiyar sa suka kawo, sabon kundin tsarin mulki ya zama wajibi kafin gudanar da kowane zabe.”
“Saboda haka, ina kira da babbar murya cewa ya kamata mu dage gudanar da zaben 2023 har sai an kafa gwamnatin rikon kwarya bayan karewar gwamnatin Buhari ta samar da sabon kundin tsarin mulkin mutane na gaskiya,” in ji shi.
Ya ce ko shakka babu duk wani zabe da aka gudanar a karkashin tsarin mulkin kasar nan zai kara dagula al’amura a kasar nan
“Babu wani zabe a karkashin wannan kundin tsarin mulkin da zai kawo matasa masu jini a jika, hazikan ‘yan Najeriya da ke son yin hidima ba tare da karbar kudi ba,” inji shi.
Ya ce sabon kundin tsarin mulkin idan aka yi shi zai samar da tsarin gwamnatin tarayya na gaskiya a maimakon tsarin shugaban kasa wanda a cewarsa yana da tsada sosai.
Shugaban gwamnatin ya yi nuni da cewa kasar za ta yi kyau a tsarin gwamnati na majalisar dokoki tare da majalisar dokoki ta Unicameral.
“Sabon tsarin mulkin ya kamata ya tanadi ‘yan majalisa na wucin gadi ba na cikakken lokaci ba inda ba za a samu albashi ba, sai dai alawus-alawus kawai,” in ji shi.