2023: Dalilin da yasa ambaton Tinubu ya cika Kafafen Yaɗa Labaru – Jigon APC, Oyalowo
Wani fitaccen dan jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Ayo Oyalowo, ya caccaki wadanda ke zargin Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, ba shi da koshin lafiya, inda ya bayyana cewa shi (Tinubu) ne ya kasance babban abin kallo a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Oyalowo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a shirin Siyasar Yau na Channels TV.
DAILY POST ta tuna cewa Tinubu ya saka wani ɗan gajeren bidiyo na kansa a kan keken motsa jiki a yammacin Lahadi don karyata jita-jita da ake yadawa cewa ba shi da lafiya sosai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Magidanci ya kashe wata Ƴar haya da wuƙa a Ondo
Ya bayyana cewa, Tinubu yana cikin labarai ne a kodayaushe domin shi ne babban abin da zai faru a zabe mai zuwa, don haka duk abin da zai yi zai zama labari.
“Na fadi a wani wuri kwanakin baya cewa batun Asiwaju Bola Tinubu shi ne babban batu a wannan zabe. Don haka duk abin da yake yi labari ne. Wasu ma har sun kai ga daukar hoton keken nasa.
“Asiwaju shine dalilin; shi ne babban al’amari a wannan zabe.
A bayyane yake, mutane za su faɗi duk abin da suke so, amma muna sane da mutumin yana buƙatar hutu na ƴan kwanaki domin matsin lambar da aka yi masa ya ɗan yi yawa.
“Ya bukaci ya huta saboda yakin neman zabe zai dade; muna da kimanin watanni hudu zuwa biyar na yakin neman zabe kafin babban zabe. Don haka ya bukaci a tabbatar da cewa bai gaji ba. Ya bukaci shan numfashin.
“Duk da haka, Tweet ya tabbatar da cewa mutumin yana cikin koshin lafiya. Suka ce yana asibiti; wasu ma sun ce ya rasu. An yi ta maganganun banza game da shi,” in ji shi.
A wani labarin kuma: Tsohon Ɗan Majalisar wakilai, Ɗaruruwan magoya bayan APC sun koma PDP a Abia
Tsohon dan majalisar tarayya kuma jigo a jam’iyyar APC, Honarabul Chinenye Ike ya koma jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Abia.
Ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta APC zuwa PDP tare da daruruwan magoya bayansa a fadin mazabar Isiala Ngwa ta Arewa da Isiala Ngwa ta Kudu a jihar Abia.