Tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu Muazu, ya bayyana kwarin guiwar jam’iyyar PDP, kan dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Babangida yace Atiku ya kamata ya lashe zaben watan Fabrairu domin Najeriya na bukatarsa.
Ya yi wannan jawabi ne a wajen kaddamar da Kwamitin tsare-tsare na tsakiya (CPC) na Jam’iyyar PDP mazaba ta 2, a dakin taro na kasa Ward 2022 National Conference, a da ke Abuja, ranar Talatar nan.
Tsohon gwamnan ya ja kunnen kwamitin kan karkatar da hankali, yana mai jaddada cewa su ci gaba da mai da hankali.
Ya bukaci kwamitin da ya yi watsi da kudi yayin da suke yakin neman zaben nasarar Atiku.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/shugaban-ghana-ya-karyata-wasikar-da-ya-nemi-tinubu-ya-baiwa-peter-obi-dama/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Tsohon gwamnan ya ce ya kamata ‘yan kwamitin su je su yi wa Atiku yakin neman zabe.
A cewar Babangida: “Na yaba wa W2W bisa aikin da kuke yi. Ya zuwa yanzu ku ne ginshiƙi kuma ƙungiyar goyon bayan jam’iyyar kuma muna alfahari da ku.
“Manufar wannan yakin shine Atiku ya lashe zabe a watan Fabrairun badi.
“Muna son Atiku ya yi nasara, amma muna da abubuwa da yawa da za mu yi don tabbatar da hakan.
“Al’ummar nan na bukatar Atiku. Ku je zuwa rumfunan zabe ku isar da saƙon kwarin gwiwa.
“Kada ku damu da ‘yan haushin nan da can. Kada ku shagala amma ku mai da hankali.”
(DAILPOST)