Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba zai dogara da tsarin kiwon lafiyar Najeriya don amfanin kansa ba idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023,Daily Post ta rawaito.
Atiku ya bayyana cewa cibiyoyin kiwon lafiya da ke kula da lafiyar sa na iya zama ba za’a same su a Najeriya ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Obasanjo: Man Fetur Ba Zai Iya Ciyar Da Al’ummar Najeriya Gaba Ba
Da yake jawabi a muhawarar gidan talabijin na Arise TV, Atiku ya koka da cewa tsarin kiwon lafiyar Najeriya yana da iyaka.
An tambayi tsohon mataimakin shugaban kasar ko zai yi amfani da cibiyoyin kiwon lafiya na Najeriya a matsayinsa na shugaban kasa don kawar da amfani da asibitocin kasashen waje.
Ya ce: “Muna da iyakoki; mun san muna da wadancan iyakoki, wuraren kiwon lafiya da ke kula da lafiyata ba za su samu ba a Najeriya.”
Atiku dai yana zaune ne a Dubai, kuma yana zuwa Najeriya ne kawai don wasu muhimman bukukuwa da harkokin siyasa.
A wani labarin kuma, Lafiya: Najeriya Na Bukatar Likitoci Dubu 12,000 A Duk Shekara – MDCAN
Kungiyar masu ba da shawara kan harkokin kiwon lafiya ta Najeriya, MDCAN, da kungiyar likitocin Najeriya, NMA, a karshen makon da ya gabata sun yi wani nazari kan harkar kiwon lafiya a kasar.
Yayin da MDCAN ta ce Najeriya za ta bukaci likitoci 12,000 a duk shekara domin magance matsalolin lafiya a kasar yadda ya kamata, NMA ta yi nuni da cewa, za ta dauki kasar akalla shekaru 25 kafin ta cimma manufa ta na likitoci 333,334 don magance matsalolin kiwon lafiyar ‘yan Najeriya.
Ku tuna cewa a halin yanzu fannin kiwon lafiya na fama da matsalar tabarbarewar kwakwalwa, idan aka yi la’akari da yawan likitoci da ma’aikatan jinya da suka yi kaura zuwa kasashen waje domin neman wuraren aiki, lamarin da ya kai adadin likitocin 10,000: 1, sabanin yadda likitoci 600 zasu ba da shawarar ga majiyyaci daya, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ayyana.