Gabanin babban zaben 2023, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, a ranar Talatar nan, ya bayyana cewa baya son hada kai da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, yana mai jaddada cewa aikin sa shi ne tallata dan takarar shugaban kasa jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a yankin Kudu maso Gabas.
Uzodinma ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels cikin shirin Politics Today.
Ya yi nuni da cewa akwai ‘ya’yan jam’iyyar APC da dama a yankin Kudu maso Gabas masu ‘biyayya’ ga jam’iyyar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Uzodinma ya ce, “Ni dan siyasa ne kuma jam’iyya ta APC ce kuma ina da dan takara na a jam’iyyar. Kuma na san muna tuntuba da magana da jama’armu domin su zabi dan takararmu.
“Na damu da yi wa jam’iyyata yakin neman zabe. Ba na son shiga cikin batutuwan Peter Obi, wanda kuka san ba dan jam’iyyata ba ne. Amma na san ’yan APC masu biyayya ne ga APC.”
Gwamnan ya kara da cewa, “Ina da yakinin cewa masu hankali a jihar Imo za su zabi jam’iyyata. A 2021, na zo nan a matsayin gwamna, kashi 99% na manyan titunan mu ba a bi. A yau an gudanar da manyan hanyoyin tattalin arziki a jihar Imo a matakin farko wanda hatta ‘yan jam’iyyar adawa suna yaba kokarina.
“Daga 1999 zuwa yau ‘yan majalisar dokokin Imo ba su da wurin zama a jihar. Sun kasance a sakatariyar karamar hukuma daya a nan Owerri. Ginin majalisar dokokin Imo da aka yi watsi da shi shekaru da yawa an sake gyara shi”.