Gboyega Akosile, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas, ya yi alfaharin cewa gwamnoni 17 da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC sun fito cikin kankanin lokaci domin ganawa da jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Tinubu. .
Akosile ya yi ikirarin cewa Tinubu ya aika gayyatar ne a safiyar yau Litinin, amma duk gwamnonin sun hallara duk da aike musu gayyatar cikin kankanin lokaci.
A cewarsa, hakan ya nuna cewa Tinubu ne kan gaba kan takaran Shugaban kasa.
“Ya aika da gayyatar taro a safiyar yau, amma gwamnoni 17 sun amsa gayyatar sa!”
Taron ya gudana ne a gidan Tinubu dake Abuja, jim kadan bayan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Sanarwar da Osinbajo ya yi na nufin zai kara da Tinubu a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.
Haka kuma mataimakin shugaban kasar ya gana da gwamnonin kafin ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasan