Daruruwan malaman addinin Musulunci da masu haddar Alkur’ani ne suka gudanar da taron addu’o’i na musamman domin ganin an samu zaman lafiya a kasar nan, tare da yi wa Gwamna Yahaya Bello addu’a ya tabbatar masa da burinsa na shugaban kasa a 2023.
Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, a yayin taron addu’o’in da aka gudanar a Kano, a ranar Lahadi ne aka yi tsokaci kan maganar Gwamna Yahaya Bello wanda a cewar masu shirya taron na nuni da cancantar sa na zama shugaban da za a zaba a zabe mai zuwa.
Malam Zakariyya Ishaq, wanda ya yi jawabi a wajen taron addu’o’in na musamman ya ce babban makasudin taron shi ne yi wa kasa addu’a tare da kuma rokon Allah Ya sa Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya zama shugaban kasa na gaba a Najeriya.
“Shi shugaba ne mai kirki, wanda hankalinsa ke cike da tausayi da jin kai ga talakawansa da kuma taimako, in ji malamin.
Mallam Ishaq ya kara da cewa Gwamna Yahaya Bello shi ne shugaba daya tilo a fadin tarayyar kasar da ya tsaya cak, ya ki amincewa da matsin lambar gwamnatin tarayya na kulle jihar sa a lokacin barkewar annobar COVID-19 ta farko.
Ya ce, a lokacin barkewar cutar, ‘yan Najeriya da yawa sun sha wahala mai yawa, amma gwamna Bello ya yi la’akari da girmansa, kofar jiharsa a bude take kuma ba a takaita zirga-zirgar jama’a a ciki ba.
Ishaq ya yi nuni da cewa matakin Gwamna Bello na wancan lokacin yana daga cikin iya jagoranci, wanda ke nufin biyan bukatun al’ummarsa cikin tausayi.
Mallam Abu Ahmed ya ce Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yana bin dabarunsa na zahiri da na shugabanci, ya cancanci ya samu dukkanin goyon bayan da ake bukata domin cimma burinsa na gaggawa na mika masa rigar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
“Don haka ne muka taru a yau domin yi masa addu’a da kuma dorewar zaman lafiya a kasar nan,” in ji shi.
Abu Ahmed ya ci gaba da jaddada cewa a addinance an koyar da mu cewa ya fi dacewa a zabi shugaba na kwarai, mai kokari sosai da zaben shugaban rikon amana.
Yanzu, yayin da bai fi shekara guda a gudanar da babban zaɓe ba, ‘yan siyasa a faɗin tarayyar sun fara neman goyon bayan zaɓe ko sake zaɓe.