2023: Dole ne a daina kashe Ƴan Arewa a Kudu maso Gabas – Dattawan Arewa
Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Dattawan Arewa NEF, Hakeem Baba-Ahmed, ya fitar da gargaɗi kan kashe ƴan Arewa a yankin Kudu maso Gabas.
Baba-Ahmed ya ce kai hari da kashe ƴan Arewa a yankin Kudu maso Gabas yana da haɗari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kaduna: Matan Ƴan Sanda sun gudanar da Azumi, addu’o’i kan hare-haren Ƴan Bindiga
Ya yi nuni da cewa irin wannan mataki na iya dagula dangantakar al’umma a wasu sassan Najeriya.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, kakakin NEF ya ce ya kamata ƴan siyasa masu neman kuri’a su fito fili su yi Allah-wadai da irin waɗannan ayyuka.
Ya kuma jaddada cewa dole ne a daina irin wannan ga ƴan Arewa.
Baba-Ahmed ya rubuta: “Ya kamata a yi Allah-wadai da hari da kashe-kashen da ake yi wa ’yan Arewa, musamman a Kudu maso Gabas, kuma a daina.
“Yana da matukar hadari domin zai iya kawo tabarbarewar dangantakar al’umma a wasu sassan Ƙasar nan.
“Muna bukatar mu ji karara da kuma yin Allah wadai daga masu son kuri’un mu