By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Bauchi kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Bala Mohammed ya ce zai yi takara ne domin ceto dimokuradiyya daga rugujewa, inda ya kara da cewa idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023, zai tabbatar da raba ayyukan yi cikin adalci a fadin kasar nan.
Mohammed, wanda tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya ne, ya tuna cewa a lokacin da yake rike da madafun iko a babban birnin tarayya Abuja, ya samu damar kafa gwamnatin hadin kai da ba a bar kowa a baya ba, wanda hakan ya sa suka samu nasarori a kowane fanni.
Mai fatan zama Shugaban kasan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar a Kaduna ranar Asabar, gabanin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar da za a yi nan gaba a watan da muke ciki.
Ya kuma bayyana cewa ya fito takara ne domin kwato dimokaradiyya daga jam’iyyar APC a halin yanzu, yana mai cewa, “Na yi takara ne saboda dole ne mu kwato dimokuradiyyarmu.
Ya yi nuni da cewa, akwai ayyuka da dama a kasar nan da ya kamata a raba tare da nuna gaskiya da adalci ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba, yana mai tabbatar da cewa da zarar an zabe shi shugaban kasa zai yi abin da ya dace.
Ya ce “Kaduna ita ce gadona ta al’adu da banbance-banbance. Na yi aiki da mutane daga sassa daban-daban na ƙasar kuma hakan ya ba ni damar yin tafiye-tafiye a cikin ƙasar. Ina takara ne saboda dole ne mu kwato dimokaradiyyar mu.
“Mun mutunta kowane mutum a lokacin da nake Ministan Babban Birnin Tarayya kafin in zama Gwamna. Haka kuma, na fito da kowa daga kowane bangare, ba tare da la’akari da bambance-bambancen da ke tsakaninmu ba, kuma a sakamakon haka, an samu zaman lafiya da ci gaba a lokacin da nake aiki a FCT.
“Muna bukatar mu fahimci kanmu a matsayin al’umma. Na koyi abubuwa da yawa a FCT a matsayina na Minista. Mun kafa gwamnatin gamayya. Ba a bar kowa abaya ba. Mun inganta fannin kiwon lafiyar mun gina asibitoci da yawa, mun gina makarantu da dama don mutane don karfafa wa wadanda ke yankunan karkara kwarin gwiwa da dakile cutar da yaran da ba su zuwa makaranta. Akwai zaman lafiya akwai ci gaba.
“Muna buga kudaden kasafi ne a takarda domin a yi gaskiya da adalci. Mun bunkasa FCT da kyau ta hanyar sa ido da tantancewa. Na kuma dauki sarakunan gargajiya domin samar da zaman lafiya mai dorewa da ci gaba a lokacin da na zama Gwamnan Jihar Bauchi. Babu wani abu da za ka iya yi a Bauchi da ba zan sani ba.”
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Felix Hyat, ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da yi wa gwamnan addu’a ya cika burinsa na zama shugaban kasar nan.