2023: Dole Ngige, Nwajiuba suyi Gaggawar Sauka daga Muƙamin su — NANS
Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa tace dole Ministan Ƙwadago Chris Ngige da Ƙaramin Ministan Ilmi Chukwuemeka Nwajiuba suyi Gaggawar Sauka daga Muƙamin su, bawai neman takarar shugaban ƙasa ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Osun 2022: Jam’iyyar NNPP Ba Ta Kawance Da Kowace Jam’iyya – Odeyemi
NANS ta bayyana rashin jindaɗin ta na yadda “basu da wata nagarta a baya, ko yanzu, suke neman Kujerar Shugaban Ƙasa ba tare da jin kunya ba,” a ƙarƙashin Jam’iyar APC.
Ɗaliban sun cigaba da cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari “ya lalata darajar ofis ɗin na yadda Ngige da Nwajiuba zasu nemi gaje shi.
“Abun kunya ne na ayyana aniyar tsayawa takara, da sayen Fom ɗin Tsayawa Takara ga Ministan Ƙwadago da Ƙaramin Ministan Ilmi,” sun faɗi haka a cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar na Ogun Damilola Simeon ya Fitar
Ɗaliban sun jaddada cewa Ngige da Nwajiuba “sun kasa shawo kan matsalar yajin Aikin ASUU, duk da a ƙarƙashin Ma’aikatun su ne zasu shawo kan matsalar.