Daga Dimokuraɗiyya
Kungiyar majalisar dokoki na jihohin Nigeria 36 sun zabi Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a matsyin dan takararsu a zaben shugaban kasa na 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Bayanin hakan ya fito ne a jawabin bayan taro da kungiyar ta gudanar a Abuja.
Yan majalisar su 365 sun tabbatar da cewa Gwamnan ya ciri tuta kuma ya cancanta a duka matakan shugabancin Nigeria irin wanda kasar nan ke bukata
Zuwa yanzu dai ana iya cewa takarar Gwamna Yahaya Bello na ta kara samun tagomashi tun bayan da ya bayyana aniyarsa ta fitowa takara a 2023, mata da matasa da kungiyoyi a Kudu da Arewacin kasarnan ke fitowa suna mara masa baya a kusan kowace rana.