By Abbas Yakubu Yaura
Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan kiran da aka yi na a kafa gwamnatin rikon kwarya bayan shudewar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a 2023 domin ba da damar rubuta sabon kundin tsarin mulki.
Aare Afe Babalola, wanda ya kafa kuma shugaban jami’ar Afe Babalola, Ado-Ekiti, ABUAD, ya shaidawa gwamnatin Buhari cewa ta dakatar da gudanar da babban zaben 2023, ta kuma nada gwamnatin wucin gadi.
Da Dumi-duminsa: Sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi Ya Rasu Yana Da Shekaru 83
A cewar Babalola, wannan gwamnatin ta wucin gadi za ta yi amfani da lokacin da ta ke kan karagar mulki wajen tsara sabon kundin tsarin mulkin da ya dace da jama’a da gaske.
Ya ce sabon kundin tsarin mulkin da za a samar cikin watanni shida, zai magance matsalolin rashin tsaro, tattalin arziki, siyasa da sauran munanan cutuka da suka addabi al’umma.
Babban Lauyan Najeriya (SAN), ya yi wannan kiran ne a cikin tarin matsalolin tsaro, kalubalen tattalin arziki da sauran batutuwan da ke barazana ga wanzuwar kasar.
Sai dai da yake mayar da martani kan hakan, mai ba shugaba Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Femi Adesina, wanda ya bayyana a gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba da izinin kafa gwamnatin wucin gadi ba.
“A iya iyakar sanina, ba ya cikin tsarin mulkinmu a kafa gwamnatin wucin gadi,” in ji Adesina.