2023: Har yanzu APC bata yanke shawarar inda zata bada Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa ba — Adamu
Jam’iyyar APC a ranar Juma’a a Abuja, tace har yanzu bata yanke shawara akan yankin daya kamata ta bada tikitin Takarar Shugaban Ƙasa ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda Sun Hallaka Ɗan Ta’adda, Bayan Daƙile Harin Ta’addanci A Katsina
Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa Sanata Adamu Abdullahi ya bayyana haka ga Manema labaru jim kaɗan bayan ya gabatar da Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Ekiti a zaɓe mai zuwa Biodun Oyebanji ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Villa, Abuja.
A lokacin da aka tambaye akan inda Shugabancin Jam’iyyar zai bada tikitin Takara, Adamu yace wannan yanke hukuncin yafi ƙarfin Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar kuma yafi Jam’iyyar, wanda ya bayyana cewar yafi shi, shi kan sa..
A cewar sa “a yau na samu damar zama Shugaban Ƙasa. Jam’iyyar tafi Ƙarfi na. Jam’iyyar har yanzu bata yanke hukunci ba, kuma bazan iya faɗin abinda Jam’iyyar zata yi ba.”
Adamu ya samu rakiyar Gwamnan Ekiti kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya Dr Kayode Fayemi, Gwamnan Jahar Kebbi kuma Shugaban Gwamnonin Jam’iyyar APC Atiku Bagudu, da Sakataren Jam’iyar APC Sanata Iyiola Omisore.
Comments 1