Jam’iyyar APC ta ce har yanzu jam’iyyar ba ta dau wani mataki a kan raba Mukamai ga yankunan dake fanin kasar nan ba, a babban zaben shekarar 2023.
Shugaban kwamitin riko/CECPC na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba ta hannun babban daraktan yada labaransa Mista Mamman Mohammed.
Ya ce Mukaman da ake zargin cewa, Jam’iyar ta fitar ga dukkannin yankunan kasar nan karya ce, tsagwaranta, juma’a mara tushe balantana Makama, kana Kuma ya Nisanta jam’iyar da wannan karyar.
Buni ya yi zargin cewa sanarwar da aka ce jam’iyyar APC ce ta yi domin tsara Mukamai ga shiya-shiya tunani ne kawai na Wani Marubuci, Wanda ba shi da alaka da shi da jam’iyyar.
Ya ce: “An jawo hankalin Mai Girma Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban Kwamitin Tsare-Tsare na Jam’iyyar APC Mai Mala Buni ga kafafen yada labarai tare da zargin cewa shi ne ya sanar da Mukaman ga shiyya-shiyya.”
“Shugaban kwamitin ya ce jam’iyyar ba ta dauki wani mataki ba a kowane fanni kan wani abu da ya shafi raba Mukaman Ofisoshi,” in ji sanarwar.
Buni ya bukaci jama’a da su yi watsi da jerin sunayen da ake zargin, yana mai cewa yaudara ce kuma kwata-kwata karya ce.