2023: In ka isa kayi Gangami irin wanda muka yi a Kano – Ganduje ya ƙalubalanci Kwankwaso
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a ranar Litinin ya kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabi’u Kwankwaso da ya gudanar da wani taro a jihar domin gwada farin jininsa.
Ganduje ya yi magana ne kan yawan fitowar jama’a a taron gangamin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka yi wa Bola Tinubu a jihar a safiyar ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Akwai Buƙatar Gaggauta Nazari Kan Ƙaruwar Yan Najeriya – Gbajabiamila
A cewar Gwamnan, da yawa daga cikin mabiya Kwankwaso a yanzu suna tare da APC.
“Don haka, idan Kwankwaso yana tunanin zai iya lashe jam’iyyar, to ya gudanar da irin wannan tattaki, ya kwatanta abin da zai faru idan zai iya,” in ji Ganduje a gidan talabijin na Channels Television’s a Shirin Politics Today a yammacin ranar Litinin.
Gwamna Ganduje ya kara nuna shakku kan batun siyasar Ibrahim Shekarau, wanda ya bayyana cewa yana ficewa daga wannan jam’iyya zuwa waccan tare da rasa dimbin mabiyansa a wannan tafiyar.
Gwamnan ya yi imanin cewa Shekarau ya bar mafi yawan mabiyansa a jam’iyyar All Progressives Congress, NNPP kuma ya ba da shawarar cewa babu wanda ya san matakin da tsohon Gwamnan zai dauka a gaba.
A wani labarin kuma: 2023: Dalilin da yasa Atiku ba zai ci Zaɓen Shugaban Ƙasa ba – Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, Rabi’u Kwankwaso, ya caccaki Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, yana mai cewa duk jam’iyyar da ba za ta iya karɓe iko da jihohin Legas, Kano, da Ribas ba, to ta manta da zaben shugaban kasa na 2023.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wurin kaddamar da titunan cikin gida na Mgbutanwo a Emohua, jihar Ribas, bisa gayyatar gwamna Nyesom Wike.