2023: Ina Fatan Yarabawa zasu Zaɓi Tinubu — Sanwo-Olu
Gwamnan Jahar Lagos Babajide Sanwa-Olu ya bayyana fatan cewa Yarabawa zasu goyi bayan Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, Bola Tinubu.
Sanwo-Olu ya bayyana haka a ranar Litinin a bikin Ojude Oba na Shekara-Shekara na 2022 a Ijebu-Ode, Jahar Ogun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bifra: Samun Takarar Peter Obi ya taƙaita ta’addancin IPOB — Gumi
“Ina da fata da imani cewa bayarbe zai haɗa kan Najeriya a matsayin ɗaya, ”
Sanwo-Olu yace Ɗan Takarar Jami’yar APC “ya kasance ɗaya daga cikin ƴan Takarar da babu irin su a fadin nahiyar Afirka.
Gwamnan Lagos yayi nuni dacewar Ojube Oba ya tunatar dacewa shi Sahihin mutum ne.