Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bukaci majalisar dokokin kasar da ta gaggauta daukar matakin zartar da dokar laifukan zabe da ke gabanta a halin yanzu don taimakawa wajen tabbatar da sahihin zabe a babban zaben 2023 mai zuwa.
Kwamishinan INEC mai kula da yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na kasa, Festus Okoye ya kuma bukaci majalisar dokokin kasar da ta zartar da kudirin kafa kotunan tafi da gidanka domin gudanar da shari’ar nan take ga duk wanda ya aikata laifin zabe a lokacin babban zabe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: Tsohon Shugaban Jami’ar LASU, Hussein Ya Rasu Yana Da Shekaru 75
Okoye wanda ya bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da manema labarai a karshen mako a hedikwatar hukumar ta INEC, Awka, jihar Anambra, ya yi alkawarin cewa hukumar a shirye take ta baiwa al’ummar kasar sahihin zabe, na gaskiya da za’a yi a kasar nan a shekarar 2023.
Ya bayyana cewa tuni hukumar ta kammala shirin bayar da horon da ya dace ga duk jami’an zabe da jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, jami’an tsaron farin kaya da na Civil Defence, NSCDC, Daraktan hukumar tsaro ta DSS, da kuma harkokin tattalin arziki da kudi. Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, kan abin da ya kunshi laifukan zabe gabanin zaben domin tabbatar da cewa babu wani mai laifin zabe da ya tsira daga fushin doka.
Kakakin hukumar ta INEC ya bayyana cewa, a zabe mai zuwa, za a baiwa jami’an rumfunan zabe iko a karkashin kudirin dokar laifukan zabe da aka gabatar na bayar da umarni ga jami’an tsaro a rumfunan zaben su damke duk wanda aka samu da aikata laifin zabe yayin da jami’an tsaro da ke da alaka da rumfunan zabe za su kama.
“Suna da ikon kama duk mutumin da ya yi ta’adi da dokar zabe sannan a kai shi kotu domin a yi masa shari’a a yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata.”
“Ya bayyana cewa, ci gaba da yin rijistar masu kada kuri’a, CVR, ba za a tsawaita wa’adin da aka diba ba, ta yadda hukumar za ta iya gudanar da rijistar masu kada kuri’a tare da yin aiki da irin wannan a kananan hukumomi 774 da rumfunan zabe 8,809 da ke fadin kasar nan gabanin zaben.”
Zaben 2023 cikin wa’adin da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada da kuma dokar zabe ya bayyana “siyan kuri’a da ciniki” a matsayin babban kalubalen da zai iya kawo cikas ga sahihancin zabukan da ke tafe, amma ya ba da tabbacin cewa hukumar ta kammala shirye-shirye don tabbatar da cewa masu kada kuri’a ne kawai wadanda suka nuna zahiri a rumfunan zabe.
kuma na’urar Biometric Voters System, BVAS, ta tabbatar da cewa ainihin mai katin zabe na dindindin, PVC, za a ba su damar kada kuri’a.
Ya yabawa shugabannin al’umma da coci-coci, da shugabanin kungiyoyin kwadago na jihar Anambra, da kuma, sarakunan gargajiya na jihar Anambra bisa goyon bayan da suka baiwa ma’aikatan hukumar a lokacin aikin CVR.