By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta tabbatar da Bashir Sheriff Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Yobe ta arewa shiyyar C.
Hukumar zaben ta kuma raba kan ta da fitowar shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar a mazabar Sanatan Yobe ta Arewa.
A baya dai APC ta sanya sunan Lawan a tashar INEC a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar a shiyyar Yobe C.
Ko da yake a fili yake cewa Shugaban Majalisar Dattawa bai halarci zaben fidda gwani na jam’iyyar da ya samar da Machina ba, amma ikon da ke mazabar ya samu hanyar shigar da sunansa a tashar INEC.
Rahotanni sun bayyana cewa Ahmad Lawan ya nemi tsayawa takarar zama shugaban Najeriya a lokacin zaben fidda gwani, wanda a zaben daya gudana ya sha kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai lamarin ya ba ‘yan Najeriya da dama mamaki yayin da aka sauya sunan sahihin wanda ya lashe zaben fidda gwani da na Lawan da bai shiga zaben ba.
A cikin takardun da INEC ta shigar a ranar Alhamis sunan Lawan ba ya daga cikin wadanda suka shiga zaben.
Kamar yadda zaku gani a kwafin takardun
A wani labarin kuma Tsohon shugaban rundunar sojin kasar nan Laftanar Janar Yusif Tukur Buratai ya nesanta kansa da duk wata kadara da ake danganta shi da ita a yankin Wuse dake Abuja.
A baya ne dai aka samu labarin cewa jami’an hukumar ICPC sun yiwa gidan sa dake yankin na Wuse kawanya, domin dai tafiya da shi.
Buratai a wata Sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa Osuagwu Ugochukwu ESQ, ya bayyana labarin da cewa wani ƙage ne, da ake son yin amfani da shi wajen batawa mai gidan nasa suna.
A baya bayan nan dai wata jarida da ake wallafa ta a Intanet ta wallafa cewa jami’an Hukumar ICPC sun yiwa gidan Buratai dake Abuja kawanya.
Jaridar ta kara da cewa an samu kudi kimanin Naira biliyan 1.85, lokacin da suka farwa gidan tsohon shugaban rundunar sojin.
A karshe ya bukaci al’umma da suyi watsi da rahoton cewa an samu abinda ake zargin na Buratai ne, sannan kuma bashi da gida a wajen da ake ikirarin cewa hakan ya faru.