Jam’iyyar APC reshen Ƙasar Landan, ta shawarci Shuwagabancin Jam’iyyar na Ƙasa daya ɗaga zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar na ƙasa da aka shirya gudanarwa a watan 26 ga watan Fabrairu na shekarar 2022.
Jam’iyyar ta bada umarnin a cikin wata sanarwa data fitar a ranar Laraba daga Shugaban Jam’iyyar na Landan Philip Ideawor.
Ideawor ya bayyana cewar ɗaga zaɓen ya zama dole domin baiwa Gwamna Mai Mala Buni Shugaban Kwamitin Ruƙo da tsare-tsaren shirya zaɓe, ya samu nasarar sasanta rikicin wasu Fusatattun ƴaƴan Jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mahi Inyas ya musanta baiwa Ganduje haƙuri bisa ƙin halartar zikirin Kano
Shugaban Jam’iyyar na Landan ya bayyana ɗaga zaɓen, a yayinda suka bada mahimmanci akan wasu abubuwa da ake buƙata, zai tabbatar da Jam’iyyar a saman mulki a shekarar 2023.
Ideawor ya bayyana cewar “yafi dacewa idan aka ɗaga zaɓen Shuwagabannin domin baiwa Jam’iyyar samun nasarar Kwamitin tsare-tsaren Shirya zaɓe.
Sanarwar ta naƙalto Ideawor na cewa ɗaga ranar zai tabbatar da samun nasara, da halartar ƴaƴan Jam’iyyar dake Ƙasar waje, domin basu yarda suyi tafiya sau biyu ba, domin zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar.
Comments 1