By Abbas Yakubu Yaura
Jam’iyyar PDP ta kara tsawaita wa’adin sayar da fom da jadawalin ayyukanta na babban zaben shekarar 2023.
Jam’iyyar PDP a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Hon. Debo Ologunagba, a ranar Alhamis,ya fitar ya ce bayan nazarin batutuwa daban-daban da kuma matsaloli, ya kara daidaita wa’adi da kuma jaddawalin ayyuka don tsawaita kwanakin rufe sayen fom na nuna sha’awar tsayawa takara a babban zaben 2023 zuwa ranar Juma’a 22 ga watan Afrilu 2022.
FAAN Ta Mayar Da Martani Game Da Mutuwar Wata Fasinja A Filin Jirgin Saman Abuja
A cewar magatakardar yada labarai, a ƙarƙashin jadawalin da aka sake dubawa, an ƙara ranar ƙarshe don mika fom ɗin da aka riga aka kammala zuwa Litinin, 25 ga watan Afrilu, 2022.
Saboda haka, Laraba 27 ga watan Afrilu, 2022, da Alhamis 28 ga watan Afrilu, 2022, aka kebe domin tantance ‘yan takarar Majalisar Jiha da na Majalisar Dokoki ta kasa da na Gwamna.
Ya kuma bayyana cewa an sanya ranar Juma’a, 29 ga watan Afrilu, 2022, don tantance masu neman shugabancin kasar, yayin da za a gudanar da duk wani kararrakin da aka yi kan tantancewar a ranar Litinin, 2 ga watan Mayu, 2022.
Sanarwar ta kara da cewa, “A cikin jadawalin da aka sabunta, an tsayar da taron mutane na mazabu 3 na musamman a ranar Asabar 30 ga watan Afrilu, 2022, yayin da za a gudanar da taron wakilan kananan hukumomin na kasa a ranar Alhamis, 5 ga watan Mayu, 2022.
“Duk ranakun da za a gudanar da zaben fidda gwani na mukamai daban-daban sun kasance iri daya ne.
“Don Allah a lura cewa duk fom din Majalisar Jiha da aka kammala za a gabatar da su a Sakatariyar Jam’iyyar ta Jihohi daban-daban.”
Jam’iyyar PDP ta bukaci dukkan masu son tsayawa takara, masu ruwa da tsaki da kuma ‘yan jam’iyyar su yi musu jagora.