2023; Kada ku sake ku saida ƙuri’un ku, wani Dattijo Giade ya gargaɗi ƴan Najeriya
Tsohon Mamba a Hukumar Raba Dai-dai ta Najeriya Aliyu Giade ya gargaɗi ƴan Najeriya da kada su sake su sayar da ƙuri’un su a Babban zaɓe mai zuwa domin zasu lalata makomar su data Ƙasar.
Yayi wannan gargaɗin a wata tattaunawa da ƴan Jarida a lokacin buɗe ƙungiyar reshen Arewa maso Gabas, The Nigeria Agenda, Wanda ya gudana a ɗakin taro na baƙi na Bauchi a ranar Laraba.
Giade wanda shine Babban baƙo a taron, yace “bana ƙalubalantar kowa akan karɓar kuɗi akan kowa amma abunda nake ƙalubalanta shine saida ƙuri’a, kada wanda ya kuskura ya saida darajar shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Al’ummomi a Katsina sun koka kan matsalar da suke fama da’ita, sunyi kira ga Gwamnati data tallafa masu
“Abun baƙin ciki ne kaga mutane suna saida ƙuri’un su. Abun baƙin ciki ne kaga matar gida na ɗora katin ta a saman Hijabi tana neman wanda zai sayi ƙuri’ar ta Naira ɗari 500 a wurare irin su Bauchi a lokacin zaben daya wuce. Abun kunya ne.
Comments 1