Biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Lokoja a ranar Alhamis din nan ta yanke kan bacewar sunansa daga cikin jerin sunayen da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta tantance na zaben 2023, kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Matthew Kolawole ya ya sha alwashin neman hakkinsa a kotun daukaka kara.
Mai shari’a Peter H. Mallong a hukuncin da ya yanke ranar Alhamis ya yi watsi da karar Kolawole, inda ya nemi INEC ta amince da shi a matsayin dan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar APC na mazabar Kabba-Bunu da Ijumu.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mai shari’a Mallong ya bayyana cewa, hukumar zaben tana da hakkin ta tsara lokacin gudanar da dukkan ayyukanta, yana mai jaddada cewa da zarar wa’adin ya kare, kotu ba za ta iya tilasta wa hukumar zaben kara wa’adin ba.
Don haka alkalin ya yi watsi da karar nasa, saboda ba shi da hurumin tilasta wa hukumar zaben bude shafinta tare da amincewa da takarar Kolawole, da zarar lokacin da aka kayyade ya cika.
Karanta kuma: Majalisar Dokokin Jihar Kogi Ta Tsige Mataimakin Kakakinta
Sai dai jigon na jam’iyyar APC ya sha alwashin neman hakkinsa a babbar kotu inda ya yi nuni da cewa yana da kwarin guiwa da amincewar bangaren shari’a na yin adalci a kotun daukaka kara.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa Femi Olugbemi, shugaban majalisar ya umurci tawagar lauyoyin sa da su daukaka kara kan hukuncin, inda ya bukaci magoya bayansa na jam’iyyar da su kwantar da hankula su kasance masu bin doka da oda.
“Ana shirye-shiryen tunkarar kotun daukaka kara domin sake duba hukuncin da karamar kotun ta yanke kamar yadda dokar nan take mai lamba FHC/LKJ/CS/35/2022, da aka shigar domin tilastawa INEC ta dora tare da buga bayanansa kamar yadda ya kamata. ‘Dan takarar jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Kabba da Bunu da Ijumu a zaben 2023, in ji sanarwar.
Kolawole ya kara da cewa babu wani cece-kuce game da yadda ya zama wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayun 2022 a Kabba, shedikwatar mazabar da jami’an INEC da jami’an tsaro suka sanya ido sosai a kai inda ya lashe mafi rinjayen kuri’u.
Shugaban majalisar a cikin wata kara mai lamba FHC/LKJ/CS/35/2022, ya nemi kotu ta umurci jam’iyyar APC da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da su sanya bayanan sa a matsayin dan takarar da ya dace a jam’iyyar APC mai mulki a zaben fidda gwani wanda aka yi a ranar 27 ga watan Mayu, 2022 a Kabba.
Ya kara da cewa bayan da ya samu kuri’u mafi inganci, daga nan ne aka zabe shi a matsayin wanda zai wakilci mazabar kamar yadda kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na mazabar Kabba-Bunu/Ijumu ya amince da shi a zaben 2023 mai zuwa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, mai shari’a Malong ya yi watsi da karar da abokin hamayyarsa, Segun Okobatoke, wanda ya nemi kotu ta amince da shi a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka bayyana.
A wani labarin kuma: Rufa’i Hanga Ya Gaji Takarar Shekarau A Jam’iyyar NNPP
Sanata Rufa’i Sani Hanga ya lashe tikitin takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya na jam’iyyar NNPP.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Hanga ya samu tikitin ne wanda Sanata Ibrahim Shekarau ya janye daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar PDP.