Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yamma Salihu Lukman, ya bukaci jam’iyyun adawa da kada su yi tsammanin samun nasara a zaben 2023.
Lukman ya bayyana haka ne a Kaduna a wata tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma.
A cewarsa, jam’iyya mai mulki tana aiki tukuru don ganin ta samu nasara a zabe mai zuwa domin shiyyar ta APC ce.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Lukman ya ce yunkurin sasantawa da ’yan jam’iyyar da suka sami matsala yana samun sakamako mai kyau, amma akwai bukatar a kara kaimi kafin a fara yakin neman zaben.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/an-kama-wasu-jamiai-biyu-da-laifin-karkatar-da-motoci-9-na-taki-a-jihar-nasarawa/
“Mun yi aiki tukuru domin ganin jam’iyyarmu ta samu nasara a zabe mai zuwa. Babu wata jam’iyya da za ta yi tsammanin za ta lashe zaben 2023 daga shiyyar Arewa maso Yamma don kawai suna ganin za su iya yin nasara,” inji shi.
Ya bayyana cewa, domin samun nasara ga jam’iyyarsa, ana kokarin kulla alaka mai karfi da shugabancin kowace jiha.
A cewarsa, kowace jahohin da ke cikin shiyyoyin sun kafa kwamitocin sulhu, inda ya kara da cewa a matsayinsu na shugabannin yankin sun ziyarci dukkan jihohin kuma za su dawo domin ganin an sulhunta duk wanda ya samu matsala.
“Kowace jiha ta kafa wani kwamiti domin sasanta ‘ya’yanta da kuma magance rikicin. Ana samun ci gaba a duk wadannan jihohin. Daya daga cikin shawarwarin da muka dauka shi ne mu sake kai ziyara jihar domin yin sulhu. Za mu kammala sulhu kafin a fara yakin neman zabe,” inji shi.
Ya ce shiyyar ta kuma sake duba rahoton hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) dangane da batun rufe rajistar masu zabe.
Ya bayyana cewa jam’iyyar ta amince da kwamitocin su hada kai da mutanen da suka yi rajista domin karbar katin zabe na dindindin (PVCs).
(DAILY TRUST)