2023: Kasawar APC ba zai sa Gwamnonin PDP da basu yi aiki su samu Ƙuri’u ba — Wike
Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce zai zama kuskure ga Gwamnonin jam’iyyar PDP, da suka kasa samar da shugabanci na gari a jihohinsu na neman kuri’u daga masu zabe.
Ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da harabar jami’ar Emohua na jami’ar jihar Ribas, da kuma kaddamar ds rukunin gidaje ga ma’aikata, wanda gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya yi a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda Sun Gargaɗi Ɗalibai Kan Tashin hankali wajen warware al’amari
Gwamna Wike ya ce, samar da ingantattun ayyuka da shi da takwarorinsa Gwamnoni shi zai sa PDP ta samu karɓuwa a jihohinsu.
Ya ce, “Idan kowace Jiha PDP ba ta yi aiki da kyau, kar ku yi tunanin za a zabe ku ne kawai saboda APC ta gaza. Idan Jihar PDP misali Jihar Ribas ba ta yi aiki mai kyau ba, sai ka ce saboda APC ba ta yi kyau a matakin kasa ba, to jama’a za su zabe mu.
“Za su ce maka: PDP ba ta yi wani aiki na azo a gani ba. Mutane ba su fahimci hakan ba. Don haka ya kamata jam’iyya ta mutunta mu kuma ta san cewa mu ne ke yi wa jam’iyyar kamfen domin muna da abin da za mu yi amfani da shi wajen yakin neman zabe.”
A wani labarin kuma: Majalisar Dokokin Bauchi ta umarci Gwamna Bala yayi Gaggawar gyara hanyoyin da Ambaliyar Ruwa ta shafa
Majalisar Dokokin Jihar Bauchi karkashin jagorancin kakakin majalisar, Danlami Ahmed Kawule, ta yi kira ga Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed da ya gaggauta daukar matakin gyara hanyoyin da ambaliyar ruwa ta rutsa da su.
Da yake jawabi a Bauchi a ranar Larabar da ta gabata, jim kadan bayan kammala zaman majalisar Abdul Ahmad Burra, kakakin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya shaidawa DAILY POST cewa a cikin ƙudurin al’amuran da ke da muhimmanci ga jama’a, Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Disina Hon Saleh Hodi Jibir ya bukaci a gudanar da aikin gaggawa na hanyar da ta hada Adamami, Disina Jama’are da Itas/Gadau da ambaliyar ruwa ta shafa.