Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihohi Kudu maso kudu Cif Dan Orbih ya ce ficewar da wasu gwamnoni da sanatoci ke yi a Jam’iyyar tasu ba zai razana su ba har su kasa rawar gaban hantsi a shekara ta 2023.
Da yake tsokaci gane da ficewar wasu jiga-jigan Jam’iyyar da suka hada da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da na Cross River Ben Ayade da Sanata Peter Nwaoboshi gami da wasu masu karfin fada a ji a jam’iyyar, Orbih ya ce babu wata barazana da za ta hana su lashe zaben shugaban kasa a shekara ta 2023..
Ya ce wannan ba shine farau a tsalle-tsalle yayan wasu jam’iyyu ke yi a Tarihin siyasar Kasarnan, don haka banu wani abinda zai basu tsoro.
“Irin haka ya faru a zamanin jamhuriya ta farko sa’ilin su Sir Abubakar Tafawa Balewa da Cif Obafemi Awolowo” cewar Orbih.
Ya kara da cewa duk masu ficewa daga jam’iyyar tasu wasu ne kurum dake neman a wanke musu kashin dake duwawun su.