Wata Ƙungiya ƙarƙashin Ƙungiyar Tabbatar da Gaskiya da Adalci a ranar Laraba tayi kira da akai takarar shugaban Ƙasa a Cikin Jam’iyyar PDP zuwa yankin Arewa domin tabbatar da gaskiya da adalci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bayan Olusegun Obasanjo Ya Fito Daga Gidan Yari Na Gyara Shi- Abdulsalam Abubakar
“Hana wani yanki neman takarar shugaban Ƙasa a PDP abinda bai dace bane, babu gaskiya, da adalci a ciki. Bai ma dace, kuma bazai yiwu a tsarin Jam’iyya ba,” inji Ƙungiyar.
Wannan neman ya biyo bayan damuwa da ƴan Najeriya suka yi na ganin an fitar da inda za’a bada takarar shugaban Ƙasa ya zuwa yankin a shekarar 2023.
Ƙungiyar wadda tana cikin ƙarƙashin jam’iyar PDP, tace shugabancin ƙasar a lokacin da PDP ke a saman mulki ya sanya yankin kudu yayi shekaru 14, inda Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan suka daɗe a mulkin, a yayinda Shugaban Ƙasa Umaru Musa Ƴar’adua ya kasance a saman mulki na shekaru 2.
Shugaban Ƙungiyar kuma tsohon Mataimakin mai horaswa na Majalisar Wakilai ta Ƙasa Ahmed Muktar ya bayyana haka a Abuja, a cikin wata sanarwa, inda yace ya dace jam’iyyar ta yi mubaya’a ga Kwamitin Amintattu nata, wanda yace a ƙyale ɗan kowane yanki ya nemi takara.