2023: Ku Sanya Nijeriya A Gaba – Jonathan Ga Ƴan Siyasa
Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya bukaci ‘yan takara da sauran ‘yan siyasa da su rika lura da haɗin kai da walwalar ‘yan Najeriya a yakin neman zabensu da sauran ayyukan zaben 2023 mai zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an Tsaro Sun Garkame Shedikwatar Jam’iyyar NNPP
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Abuja yayin taron shekara-shekara na tunawa da ayyukan alheri na Tsohon Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida
A cewarsa, yana da kyau ga sauran ‘yan Najeriya su guji nuna halin ko-in-kula, amma su taka rawar gani a tsarin dimokuradiyyar kasar don zabar shugabannin da suka dace da za su kyautata Nijeriya da hadin kai.
“Zabuka masu zuwa na da matukar muhimmanci ga burinmu na kasa, da wadata da ci gaba. Ina kira ga ‘yan siyasarmu da su kula da hadin kanmu da zaman lafiyarmu, su kuma yi amfani da da’a wajen yakin neman zabe da sauran harkokin siyasa.
“Ga sauran mu, wannan lokacin ba ya ba mu jin daɗin halin ko-in-kula ba. Dole ne mu kuduri aniyar shiga cikin tsarin dimokuradiyyar mu. Tana bukatar mu hada kai mu zabi wadanda za su tafiyar da al’amuran kasar nan da gaskiya domin tabbatar da zaman lafiya da adalci da hadin kai da ci gaba a kasarmu,” inji Jonathan da ya yi magana kusan.
A Wani Labarin Kuma: Za’a Fuskanci Mummunan Ambaliyar Ruwa a Abuja
Hukumar Agajin Gaggawa ta Babban Birnin Tarayya (FEMA) ta sanar da Mazauna Babban Birnin Tarayya Abuja game da Ambaliyar mai ƙarfi da za’a yi a Abuja.
FEMA ta buƙaci Ma’aikatan gaggawa dasu kasance a shirye don ceto rayuka da dukiyoyi a babban birnin kasar.