Tsohon Gwamnan Jahar Ogun Gbenga Daniel yayi kira ga ƴan Najeriya dasu yi zaɓe da Ƙwaƙwalan su a Babban zaɓen Shekarar 2023.
Tsohon Gwamnan yayi jawabi ne a taron wata ƙasida na gidan rediyo karo na huɗu mai taken “Siyasar Ƴan Najeriya” a Lagos a ranar Talata.
Yayi nuni dacewar wannan itace hanya kaɗai da ƴan Najeriya zasu canja ƙaddarar Ƙasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ɗangwani, Ɗanburam, Ɗambatta da Masu Ruwa da tsakin PDP sun zargi Kwankwaso da yin Ƙarfa-Ƙarfa
Yace “Zaɓe mai zuwa (na Shekarar 2023) zai bamu damar mu sake rubuta makomar Najeriya. Abinda muka cimmawa a Shekara mai zuwa zai kasance na Shekaru 8 masu zuwa.”
Daniel ya jaddada cewa hanya kaɗai da ƴan Najeriya zasu baiwa maraɗɗa kunya shine ta hanyar zaɓar mutanen da suka san halin da suke ciki.
Tsohon Gwamnan yayi kira ga ƴan Najeriya dasu jefar da sayan ƙuri’a, tare da tambayar ƴan takarar Shugaban Ƙasa akan yadda zasu kiyaye Alƙawurran su.
“Idan wani yace zai ƙirƙiri gidan talabijin kada kayi mashi dariya, tambayar shi yadda zai gina gidan talabijin ɗin.